Friday, February 1, 2019

4G da LTE: Shin daya ne?

4G da LTE: Shin daya ne?


Daga salisuwebmaster Shugaban Makarantar Duniyar Computer
"Lokacin da kake shiga internet ta hanyar mafani da wayar hannu, iya saurin da take yi wurin bude shafuka yana yin jin dadin amfani da intanet din. Idan ana maganar 4G to magana ce ta hayar da ta fi kowace saurin bude shafuka a intanet da ake da ita domin aikawa da sakon data da musayar bayanai ta hanyar kimiyar kere-kere. To mene ne 4G din nan? Sannan mene ne LTE? Mene ne bambamci dake tsakaninsu?

Mene ne 4G?

4G shine karni na
hudu na ilimin yadda za a iya musayar bayanai ta hanyar kimiyar kere-kere na
waya, wanda aka fi sani da 4G wato (4th Generation). Shi wannan karni
Radiocommunication Standardization Sector of the International
Telecommunication Union (ITC) sune suke bayar da ka’idojin da suke son
kamfanonin da suke kirkirar wayoyi da su cika kafin ace waya takai wannan
mataki na 4G.
Kasar da tafi
shahara yanzu wacce take amfani da 4G network ita ce North America, kamfanin
Gearbest yana sayar da wayoyin masu zubin 4G. Kodayake wadansu abokanan
kasuwancinsu basa samun wannan damar kasancewar shi 4G din ba ko’ina yake ba a
wannan kasa dole sai mutum yazo wurin da akwai wannan tsari na 4G kafin ya samu
romonsa.
Mafi yawan masu
ikirarin suna bayar da 4G idan masu irin wannan wayar suke zo inda wannan
network yake sai kawai wayoyinsu su nuna musu 3G, amma babu damuwa idan wayarka
na amsar 4G duk lokacin da ka shiga wurin network mai 4G zata koma tayi amfani
da 4G mai karfi.
Musayar bayanai ta
hanyar 4G ya fi sauri sosai ga mai amfani da 3G. 4G LTE wireless broadband shi
kuma ya ninka 3G saurin musayar bayanai har sau goma. Karfin saukar da bayanai da
LTE yake yi yana kaiwa har 12Mbps, tura bayanai kuma yana kaiwa har 5Mbps,
wanda saukar da abu daga intanet yana kaiwa wani lokaci har 50Mbps. Ta bangaren
saurin aikawa da bayanai da 4G yake mafi karanci 100Mbps wanda idan mutum yana
wurin da network din yake da karfi saurin saukar da bayanai yana kaiwa 1Gbs.

Mene ne LTE?

LTE na nufin Long
Term Evaluation wanda ake rubuta shi kowane lokaci da 4G LTE. Kodayake mutane
suna daukar LTE a matsayin 4G amma shi LTE daya ne daga cikin ayyuka ko ‘ya’yan
4G, sai dai LTE muna iya saka shi a cikin sababbin karni na shiga intanet da
waya.
Shi wannan
technology na LTE wani hadin gwiwa ne na kungiyoyin samar da bayanai na
telecommunication domin ganin an kara ingantawa da samar da sauki wurin sarrafa
bayanai wanda suka kira shi da suna 3GPP ko 3rd Generation Partnership Project.
Saboda haka shi
LTE kusan cigaba ne a karfafawa GSM/UMTS wurin karbar bayanai da aikasu ta
waya, domin daman makasudin yin wannan LTE din domin a samu karfi ne wurin
aikawa da sakonni ta hanyar wireless wanda aka fi sani da Digital Signal
Processing (DSP).

LTE ba 4G ba ne

Kodayake mafi
yawan mutane da suke amfani da LTE suna tsammanin shine 4G amma a bayanan mu na
baya ya tabbatar da cewar LTE ba 4G bane.
Matsala da rudu
da aka samu tun farkon shigowar LTE shine sunan da aka saka mishi na 4G-LTE
amma inda matsalar take shine shi wannan technology na LTE bai cika sharuddan
da waccan kungiya ta International Telecommunication Union (ITU) ta shardanta
ba.
Saboda haka shi
LTE zaka iya kiran shi da kanin 4G tunda saurin shi yafi na 3G amma kuma bai
kai 4G din ba. Domin a ka’idar da ITU suka shardanta shine dole a matakin farko
sai karfin shiga da fitar bayanai na intanet yakai 100Mbps. Saboda rashin
kaiwar LTE wannan mataki kuma yafi matakin 3G shine 3GPP suka fitar da sabon ka’ida
wacce suka kirata da LTE-Advanced.

Mene ne LTE Advance

LTE advanced
kusan shine ne tsarin 4G a ka’idojin da 3GPP suka fitar. Wannan ya kara karin
yazo ne a karshen shekarar 2009, amma sai dai a lokacin shi kanshi LTE din yana
a kan zango ko karni na takwas ne a wurin yinsa wanda hakan ya samar da
sharudan da duniya ta yarda da shi, kodayake har yanzu duniyar ba ta yarda da ka’idojin
da aka daurawa LTE Advanced ba.
Shi LTE Advanced
yanzu yana karnin shi na 10 ne kuma ya hada sharudi da ka’idojin da ITU suna
sakawa 4G wanda a yanzu LTE Advanced yana kaiwa 1Gbps wurin musayar bayanai

Rufewa

A yanzu haka da
muke magana mafi yawan kamfanonin da muke amfani da su wurin shiga intanet ko
kiran waya (Internet Service Provider) suna amfani da 3G ne da LTE ne ana kuma
iya fahimtar haka ne ta alamar da yake nunawa a samar wayarka domin yana rubuta
karfin network din. Amma dai maganar 4G musamman mu da muke a Najeriya sai dai
watakila nan gaba."

Hukumar kula da albarkatun man fetur na 'kasa (NNPC) ta fitar da sanarwan cewa gobe asabar 2-2-2019 shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabbin rijiyoyin men fetur da aka samu nasaran tonawa a yankin kogin Kolmani dake karamar hukumar Alkaleri jihar Bauchi

SHUGABA BUHARI ZAI KAFA TARIHI

Datti Assalafy Ya Rubuta A Shafin Shi Na Facebook 

"Hukumar kula da albarkatun man fetur na 'kasa (NNPC) ta fitar da sanarwan cewa gobe asabar 2-2-2019 shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabbin rijiyoyin men fetur da aka samu nasaran tonawa a yankin kogin Kolmani dake karamar hukumar Alkaleri jihar Bauchi

Wannan shine karon farko a tarihin duniya da akayi nasaran tona rijiyoyin man fetur a arewa kuma a karkashin gwamnatin shugaban 'kasa Muhammadu Buhari, sannan jihar Bauchi zata shiga jerin jihohi masu arzikin man fetur a Nigeria

Wannan nasarane daga Allah, Baba Buhari mungode."

Allah Ka taimaki shugaba Buhari Ka kara masa taimako da nasara Amin Summa Amen

Thursday, January 31, 2019

YA KAMATA MU NEMI AFUWAR SHEIKH DR. AHMAD GUMI

YA KAMATA MU NEMI AFUWAR SHEIKH DR. AHMAD GUMI

Daga Datti Assalafy Yace A Naimi Afuwan Dr Gumi

"A baya can, mun kasance masu kausasa harce idan Sheikh Dr. Ahmad Gumi yayi magana akan siyasar Nigeria, a yanzu mun fahimci cewa munyi kuskure idan muna masa raddi akan abar banza siyasar Nigeria

Maganar gaskiya yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria lamari ne mai girma da rikitarwa wanda da wahala ace an kawo karshen cin hanci da rashawa, duk ta'asar da 'dan siyasa zai tabka, da duk irin cin amanar da zai aikata da satar dukiyar al'umma ko da tallafawa ayyukan ta'addanci ne, to yana dawowa cikin jam'iyyah mai mulki magana ya kare

Na taba jin Dr. Ahmad Gumi ya furta wata kalma wanda sai a yanzu ne na fahimci gaskiyar abinda ya furta, yace a batun yaki da cin hanci da rashawa karyane they are all corrupt
Duk inda mutum ya kai ga biyewa bangare daya a 'yan siyasar Nigeria to zai iya kunyata daga karshen al'amari"

Allah Ya sauwake
Amen summa Amen

Wednesday, January 30, 2019

AN GANO MEN FETUR A JAHAR BORNO DAKE YANKIN AREWA

AN GANO MEN FETUR A JAHAR BORNO DAKE 
YANKIN AREWA

Wannan Shi ne Labarin Da Sha'arraen Marubucin Nan Na Faceboo Datti Assalafy Ya Rubutu a Shafin Shi Na Facebook, Ga dai Abun Da Ya Rubuta Nan

"Yanzu naci karo da wannan labarin a kamfanin jaridar Rariya sukace:

"An gano wani waje da ke nuna alamar man Fetur a jihar Borno, an gano wajen ne a yankin Manguno dake jihar Borno. 
Wurin dai kamar famfo ne amma sai ruwan ya koma yana fitowa da maiko, wanda yake nuna akwai alamar man fetur a wajen".

Tabbas 'kasar Borno tana daya daga cikin jihohin da binciken masana albarkatun 'kasa suka gano tun shekaru masu yawa cewa akwai arzikin man fetur a yankin da sauran albarkatun 'karkashin 'kasa wanda ya hada da zinare da gwalagwalai

Yana daga cikin manufar da yasa makiya cigaba arewa da musulunci suka assasa kafuwar kungiyar Boko Haram domin kada a tono albarkatun man fetur da zinare dake kwance a gurin

Na tabaji shugaba Buhari yana jawabi yace; lokacin yana gwamnan arewa maso gabashin Nigeria ya taba zuwa har inda aka gano men fetur a wannan yanki na Manguno da shi kansa jejin sambisa an nuna masa ya gani da idonsa

Kamar yankin Tabkin Chadi wanda duk 'kasar Borno ne, akwai lafiyayyen kwantaccen 'danyen man fetur a gurin, can shekarun baya har an fara tonon man, amma wannan yanki yanzu gaba daya 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun mamayeshi, kuma har yanzu akwai kayan aikin da aka fara tonon man a yankin yana karkashin ikonsu

Duk da makircin makiya cigaban arewa muna kyautata tsammanin insha Allahu a sanadin shugaba Buhari sai an fara tono man fetur arewa, domin ana dab da fara hako man fetur a jihar Bauchi bayan an samu nasaran tona rijiyoyin

Muna rokon Allah Ya karawa yankin mu na arewa albarka Ya bamu ikon cin moriyarsu, Allah Ka tsare mana arewa daga makircin makiyanta"Labarai Cikin Hoto: Yadda Bikin Kammala Makarantar Jaruma Rahama Sadau Ya Kasance Tare Da Yan Uwanta A kasar Cypurs

Labarai Cikin Hoto: Yadda Bikin Kammala Makarantar Jaruma Rahama Sadau Ya Kasance Tare Da Yan Uwanta A kasar CypursBoko Haram: Gwamnatin Barno Ta Dauki Mafarauta Da ’Yan Tauri Aiki

Boko Haram: Gwamnatin Barno Ta Dauki Mafarauta Da ’Yan Tauri Aiki

Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima, ya ce gwamnatin sa ta tattara mafarauta da ‘yan tauri da za a ba horon shiga aikin karfafa tsaro.

Shettima, ya ce sojoji ne za su ba mafarautan horon gaugawa kafin a tura su ayyukan gadi da sa-ido a yankunan birnin Maiduguri da kewaye.

Gwamna Kashim ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi bakuncin Kwamandan dakarun Operation Lafiya Dole Benson Akinroluwo da ya kai ma shi ziyara.

Ya ce mafarautan an tattara su ne a wasu wurare na sirri, yayin da yanzu haka gwamnati na kokarin ganin ta tanadar masu duk kayayyakin aikin da ya wajaba su samu.

Kashim ya cigaba da cewa, nan da kwanaki kadan za su kaddamar da mafarautan da ‘yan tauri, wadanda za su taimaka wajen dakile ta’addanci a fadin jihar Borno.
TASIRI DA FA'IDAR ISTIGFARI DUNIYANCE DA LAHIRANCE

1-ISTIGFARI yana kawo yafiyar ALLAH 

(NUH-10)

2-ISTIGFARI yana janyo  ruwan sama marka marka 

(NUH-11)

3-ISTIGFARI yana habaka dukiya da gonaki da wadatattun ruwa da samarda nagartattun 'ya'ya (NUH-12)

4-ISTIGFARI yana dauke masifu da annoba kamar kisan kai da annoba irinsu IBOLA da ire irensu, ALLAH yace= [ALLAH bazai azabtar dasu anan duniyaba idan kai ANNABI kana cikinsu, kuma ALLAH bazai azabtar
dasu idan suna ISTIGFARI]

(ANFAL-33)

5-ISTIGFARI yana jawo Rahaman ALLAH (NAMLI-46)

6-ISTIGFARI yana sabautarda shiga ALJANNA (A/ IMRANA-135-136)

7-ISTIGFARI yana jawo adu'ar Mala'iku masu rike da al'arshi ga mai yi

8-ISTIGFARI yana tsarkake mugun magana da aiki

9-ISTIGFARI yana sanya mai yinsa acikin ma'abota dama a Qiyama

10-ISTIGFARI yana jawo kyakkyawar busharar Mala'iku ga mai yinta yayin mutuwarsa

11-ISTIGFARI yana kawarda bakin ciki da damuwa

12-ISTIGFARI yana kara fikira da imani

13-ISTIGFARI yana jawo kaunar ALLAH da farin cikinsa ga maiyi samada farin cikin wanda yaga
mutuwa da idonsa kuma yatsira daga gareta

14-mai ISTIGFARI yana samun ɗanɗanon imani da ɗa'a

15-ISTIGFARI yana gusarda zaman kaɗaici da shiru tsakanin bawa da Mahaliccinsa