Wednesday, January 30, 2019

AN GANO MEN FETUR A JAHAR BORNO DAKE YANKIN AREWA

AN GANO MEN FETUR A JAHAR BORNO DAKE 
YANKIN AREWA

Wannan Shi ne Labarin Da Sha'arraen Marubucin Nan Na Faceboo Datti Assalafy Ya Rubutu a Shafin Shi Na Facebook, Ga dai Abun Da Ya Rubuta Nan

"Yanzu naci karo da wannan labarin a kamfanin jaridar Rariya sukace:

"An gano wani waje da ke nuna alamar man Fetur a jihar Borno, an gano wajen ne a yankin Manguno dake jihar Borno. 
Wurin dai kamar famfo ne amma sai ruwan ya koma yana fitowa da maiko, wanda yake nuna akwai alamar man fetur a wajen".

Tabbas 'kasar Borno tana daya daga cikin jihohin da binciken masana albarkatun 'kasa suka gano tun shekaru masu yawa cewa akwai arzikin man fetur a yankin da sauran albarkatun 'karkashin 'kasa wanda ya hada da zinare da gwalagwalai

Yana daga cikin manufar da yasa makiya cigaba arewa da musulunci suka assasa kafuwar kungiyar Boko Haram domin kada a tono albarkatun man fetur da zinare dake kwance a gurin

Na tabaji shugaba Buhari yana jawabi yace; lokacin yana gwamnan arewa maso gabashin Nigeria ya taba zuwa har inda aka gano men fetur a wannan yanki na Manguno da shi kansa jejin sambisa an nuna masa ya gani da idonsa

Kamar yankin Tabkin Chadi wanda duk 'kasar Borno ne, akwai lafiyayyen kwantaccen 'danyen man fetur a gurin, can shekarun baya har an fara tonon man, amma wannan yanki yanzu gaba daya 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun mamayeshi, kuma har yanzu akwai kayan aikin da aka fara tonon man a yankin yana karkashin ikonsu

Duk da makircin makiya cigaban arewa muna kyautata tsammanin insha Allahu a sanadin shugaba Buhari sai an fara tono man fetur arewa, domin ana dab da fara hako man fetur a jihar Bauchi bayan an samu nasaran tona rijiyoyin

Muna rokon Allah Ya karawa yankin mu na arewa albarka Ya bamu ikon cin moriyarsu, Allah Ka tsare mana arewa daga makircin makiyanta"2 comments:

  1. Kai alhamdulillahi baba buhari Allah ya kara taimako

    ReplyDelete
  2. Masha Allah tabarakallah.
    Ubangiji Allah ya taimaki Baba Buhari

    ReplyDelete