Wednesday, January 30, 2019

Boko Haram: Gwamnatin Barno Ta Dauki Mafarauta Da ’Yan Tauri Aiki

Boko Haram: Gwamnatin Barno Ta Dauki Mafarauta Da ’Yan Tauri Aiki

Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima, ya ce gwamnatin sa ta tattara mafarauta da ‘yan tauri da za a ba horon shiga aikin karfafa tsaro.

Shettima, ya ce sojoji ne za su ba mafarautan horon gaugawa kafin a tura su ayyukan gadi da sa-ido a yankunan birnin Maiduguri da kewaye.

Gwamna Kashim ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi bakuncin Kwamandan dakarun Operation Lafiya Dole Benson Akinroluwo da ya kai ma shi ziyara.

Ya ce mafarautan an tattara su ne a wasu wurare na sirri, yayin da yanzu haka gwamnati na kokarin ganin ta tanadar masu duk kayayyakin aikin da ya wajaba su samu.

Kashim ya cigaba da cewa, nan da kwanaki kadan za su kaddamar da mafarautan da ‘yan tauri, wadanda za su taimaka wajen dakile ta’addanci a fadin jihar Borno.

No comments:

Post a Comment