Friday, February 1, 2019

4G da LTE: Shin daya ne?

4G da LTE: Shin daya ne?


Daga salisuwebmaster Shugaban Makarantar Duniyar Computer
"Lokacin da kake shiga internet ta hanyar mafani da wayar hannu, iya saurin da take yi wurin bude shafuka yana yin jin dadin amfani da intanet din. Idan ana maganar 4G to magana ce ta hayar da ta fi kowace saurin bude shafuka a intanet da ake da ita domin aikawa da sakon data da musayar bayanai ta hanyar kimiyar kere-kere. To mene ne 4G din nan? Sannan mene ne LTE? Mene ne bambamci dake tsakaninsu?

Mene ne 4G?

4G shine karni na
hudu na ilimin yadda za a iya musayar bayanai ta hanyar kimiyar kere-kere na
waya, wanda aka fi sani da 4G wato (4th Generation). Shi wannan karni
Radiocommunication Standardization Sector of the International
Telecommunication Union (ITC) sune suke bayar da ka’idojin da suke son
kamfanonin da suke kirkirar wayoyi da su cika kafin ace waya takai wannan
mataki na 4G.
Kasar da tafi
shahara yanzu wacce take amfani da 4G network ita ce North America, kamfanin
Gearbest yana sayar da wayoyin masu zubin 4G. Kodayake wadansu abokanan
kasuwancinsu basa samun wannan damar kasancewar shi 4G din ba ko’ina yake ba a
wannan kasa dole sai mutum yazo wurin da akwai wannan tsari na 4G kafin ya samu
romonsa.
Mafi yawan masu
ikirarin suna bayar da 4G idan masu irin wannan wayar suke zo inda wannan
network yake sai kawai wayoyinsu su nuna musu 3G, amma babu damuwa idan wayarka
na amsar 4G duk lokacin da ka shiga wurin network mai 4G zata koma tayi amfani
da 4G mai karfi.
Musayar bayanai ta
hanyar 4G ya fi sauri sosai ga mai amfani da 3G. 4G LTE wireless broadband shi
kuma ya ninka 3G saurin musayar bayanai har sau goma. Karfin saukar da bayanai da
LTE yake yi yana kaiwa har 12Mbps, tura bayanai kuma yana kaiwa har 5Mbps,
wanda saukar da abu daga intanet yana kaiwa wani lokaci har 50Mbps. Ta bangaren
saurin aikawa da bayanai da 4G yake mafi karanci 100Mbps wanda idan mutum yana
wurin da network din yake da karfi saurin saukar da bayanai yana kaiwa 1Gbs.

Mene ne LTE?

LTE na nufin Long
Term Evaluation wanda ake rubuta shi kowane lokaci da 4G LTE. Kodayake mutane
suna daukar LTE a matsayin 4G amma shi LTE daya ne daga cikin ayyuka ko ‘ya’yan
4G, sai dai LTE muna iya saka shi a cikin sababbin karni na shiga intanet da
waya.
Shi wannan
technology na LTE wani hadin gwiwa ne na kungiyoyin samar da bayanai na
telecommunication domin ganin an kara ingantawa da samar da sauki wurin sarrafa
bayanai wanda suka kira shi da suna 3GPP ko 3rd Generation Partnership Project.
Saboda haka shi
LTE kusan cigaba ne a karfafawa GSM/UMTS wurin karbar bayanai da aikasu ta
waya, domin daman makasudin yin wannan LTE din domin a samu karfi ne wurin
aikawa da sakonni ta hanyar wireless wanda aka fi sani da Digital Signal
Processing (DSP).

LTE ba 4G ba ne

Kodayake mafi
yawan mutane da suke amfani da LTE suna tsammanin shine 4G amma a bayanan mu na
baya ya tabbatar da cewar LTE ba 4G bane.
Matsala da rudu
da aka samu tun farkon shigowar LTE shine sunan da aka saka mishi na 4G-LTE
amma inda matsalar take shine shi wannan technology na LTE bai cika sharuddan
da waccan kungiya ta International Telecommunication Union (ITU) ta shardanta
ba.
Saboda haka shi
LTE zaka iya kiran shi da kanin 4G tunda saurin shi yafi na 3G amma kuma bai
kai 4G din ba. Domin a ka’idar da ITU suka shardanta shine dole a matakin farko
sai karfin shiga da fitar bayanai na intanet yakai 100Mbps. Saboda rashin
kaiwar LTE wannan mataki kuma yafi matakin 3G shine 3GPP suka fitar da sabon ka’ida
wacce suka kirata da LTE-Advanced.

Mene ne LTE Advance

LTE advanced
kusan shine ne tsarin 4G a ka’idojin da 3GPP suka fitar. Wannan ya kara karin
yazo ne a karshen shekarar 2009, amma sai dai a lokacin shi kanshi LTE din yana
a kan zango ko karni na takwas ne a wurin yinsa wanda hakan ya samar da
sharudan da duniya ta yarda da shi, kodayake har yanzu duniyar ba ta yarda da ka’idojin
da aka daurawa LTE Advanced ba.
Shi LTE Advanced
yanzu yana karnin shi na 10 ne kuma ya hada sharudi da ka’idojin da ITU suna
sakawa 4G wanda a yanzu LTE Advanced yana kaiwa 1Gbps wurin musayar bayanai

Rufewa

A yanzu haka da
muke magana mafi yawan kamfanonin da muke amfani da su wurin shiga intanet ko
kiran waya (Internet Service Provider) suna amfani da 3G ne da LTE ne ana kuma
iya fahimtar haka ne ta alamar da yake nunawa a samar wayarka domin yana rubuta
karfin network din. Amma dai maganar 4G musamman mu da muke a Najeriya sai dai
watakila nan gaba."

No comments:

Post a Comment